Mogherini ta shigo birnin Tehran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i3943-mogherini_ta_shigo_birnin_tehran
A safiyar yau, Shugabar siyarar wajen kungiyar tarayyar Turai ta safka a birnin Tehran
(last modified 2018-08-22T11:28:08+00:00 )
Apr 16, 2016 05:35 UTC
  • Mogherini ta shigo birnin Tehran

A safiyar yau, Shugabar siyarar wajen kungiyar tarayyar Turai ta safka a birnin Tehran

Madam Federica Mogherini za ta tattauna da manyan jami'an gwamnatin Iran kan batutuwa dadaban daban, daga cikin wadanda za ta tattauna da su, Muhamad Jawad Jarif Ministan harakokin wajen kasar, Ali Larijani, kakakin Majalisar dokoki sai kuma Ali Shamkhani babban saktaren Majalisar koli t tsaron kasar Iran.

Tattaunawar za ta fi meda hankali ne kan fadada alakar kasuwanci tsakanin kasashen Turai da Jumhoriyar musulinci ta Iran, samar da ofishin kungiyar tarayyar Turai a nan birnin Tehran tare kuma da yin nazari kan batutuwan dake hana ruwa gudu kan zartar da yarjejjeniyar shirin nukiyar Iran na zaman lafiyar da aka cimma.

Baya ga haka ana sa ran bangarorin biyu za su cimma yarjejjeniyar kan kasuwancin Man fetur tare da makamashi.

Rahoton ya ce daga cikin tawagar Shugaban siyasar wajen kungiyar Tarayyar Turai a kwai kwamishinoni na bangaren harakokin siyasar EU guda bakwai.