Sabanin Iran da Saudiya riba ce ga Haramcecciyar kasar Isra'ila
Shugaban Majalisar Fayyace tsarin milki na Iran ya ce Sabanin Kasashen Iran da Saudiya riba ce ga haramcecciyar kasar Isra'ila
Yayin da yake ishara kan sabanin dake ci gaba da kasancewa tsakanin kasashen Iran da Saudiya ,Ayatu..Akbar Hashimi Rafsanjani Shugaban Majalisar Fayyace tsarin milki na Iran ya ce hadin kai tsakanin kasashen guda biyu shi kadai ne zai iya daukaka kasashen musulinci a idanun Duniya, domin a halin da ake cikin kasashen na musulmi sun yi rauni a Duniya kuma babu wani da yake cin ribar wannan sabani face haramcecciyar kasar Isra'ila.
Yayin da yake bayyana damuwarsa kan sanya kungiyar Hizbull..ta kasar Lobnon a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda ya ce wannan wani tsararen shiri ne domin karfafa Gwamnatin Haramcecciyar kasar Isra'ila.
A bangare guda Ayatul..Rafsanjani ya tabo batun yarjejjeniyar da kasar Iran ta cimma da manyan kasashen Duniya kan shirin nukiyarta na zaman lafiya, inda ya ce ba shakka jami'an Diplomasiyar kasar na iya kokarinsu wajen kare haki da kuma amfanin Al'ummar Iran .