Ganawar Mataimakin Ministan Harakokin wajen Iranda Shugaban Kungiyar Hizbul...
Mataimakin Ministan Harakokin wajen Iran mai kula da kasashen Larabawa gami da kasashen Afirka tare shugaban kungiyar Hizbul..na kasar Labnon sun gana tare da tattauna kan abinda ke faruwa a Palastinu, Labnon musaman kan batun siriya
A ganawartasa da Shugaban kungiyar Hizbul...Sayid Hasan Nasrull..., Husain Amir Ilahiyan Mataimakin Ministan Harakokin wajen Iran ya bayyana ban girma ga wadanda suke yi shahada a fagen yakin da HKI gami da kungiyoyin 'yan ta'adda a wannan Lahadi, inda ya kara da cewa ba don sadaukar da kai na shahidai ba wajen kalubalantar HKI da 'yan ta'adda ,da yanzu babu wani sauran tsaro a yankin.
A yayin da yake suka kan masu son sanya rarrabuwar kawuna tsakanin musulmi, Shugaban kungiyar Hizbul..Sayid Hasan Nasrul..ya ce wajibi Duniyar musulmi suka zamanto masu basira kan take-taken Haramcecciyar kasar Isra'ila.
Sayid Hasan Nasrul..ya kara da cewa ta'addancin da 'yan ta'addar Takfiriya ke yi a kasashen siriya da iraki tare da kokarin sanya hargizi na tashin hankali a sauren kasashen musulmi na yankin na gudana ne bisa tsarin bakar siyasar Haramcecciyar kasar Isra'ila da kasashe maso goya mata baya.
Yayin da ya koma kan kimshikin siyasar Jumhoriyar musulinci ta Iran a yakin da 'yan ta'adda tare da taimako wajen magance rikicin siyasar yankin, Sayid Hasan Nasrull...ya ce bangarorin dake amfani da karfin soja gami da 'yan ta'adda domin cimma manufofinsu da kuma kare kujerar milkinsu da Haramcecciyar kasar Isra'ila sune sanadiyar billar tashin hanhali da bunkasar 'yan ta'adda a yanki.
A nasa Bangare Husain Amir Ilahiyan Mataimakin Ministan Harakokin wajen Iran ya meka ta'aziyarsa ga iyalai da kuma Shugaban kungiyar Hizbul....dangane da Shahadar Mustapha Badrudin daya daga cikin Shugabanin kuma babban kwamandan kungiyar gwagwarmaya ta hizbull...wanda ya yi shahada a jijifin safiyar ranar Juma'a a birnin Damuscus fadar milkin kasar Siriya