Iran Zata Iya Neman Diyya Wajen Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i5299-iran_zata_iya_neman_diyya_wajen_amurka
Majalisar dokokin Iran ta amunce a wannan Talata da wata doka da zata cilastawa gwamnatin kasar neman diyya wajen Amurka saboda aikata mata da laifuka cikin shekaru 63.
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 17, 2016 07:31 UTC
  • Iran Zata Iya Neman Diyya Wajen Amurka

Majalisar dokokin Iran ta amunce a wannan Talata da wata doka da zata cilastawa gwamnatin kasar neman diyya wajen Amurka saboda aikata mata da laifuka cikin shekaru 63.

Doka dai ta ce gwamnatin nada yaunin daukan duk matakan da suka dace domin biyyan diyya akan duk laifukan da Amurka tayi mata, ko ga kaddarori, ko kuma al'ummar ta, tun bayan juyin mulkin gwamntin lokacin Mohammad Mossadegh a shekara 1953 da kuma yakin Iran-Irak.

kawo yanzu Iran din bata bayyana adadin diyya dake bukata ba, aman ma'taimakin shugaban harkokin majalisar dokokin kasar Majid Ansari, ya bayana a wata muhawara cewa tuni wasu kotinan Iran suka bukaci Amurka data biya kasar diyya ta $ miliyan 50.