An Kawo Karshen Gasar Karatun Alkur'ani Karo Na 33 A Nan Tehran
A yammacin yau ne aka kawo karshen gasar karatun Alkur'ani mai girma karo na 33 da aka gudanar da shi a nan Iran inda aka rarraba kyaututtuka ga makaranta da mahaddata Alkur'ani mai girma da suka nuna bajinta a bangarorin da suka yi gasar.
An fara gudanar da bikin rufe gasar karatun Alkur'anin na bana ne wanda aka gudanar da shi a babban Musallan marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke nan Tehran da jawabin da Hujjatul Islam Sayyid Mustafa Husaini, babban sakataren gasar karatun Alkur'ani mai girma din karo na 33, inda yayi karin bayani kan irin ayyukan da aka gudanar da kuma tsare tsare da aka yi tsawon kwanaki shida da aka yi ana gudanar da gasar.
Har ila yau daga cikin bukukuwan da aka gudanar a yau din sun hada da sanar da wadanda suka nuna bajinta a yayin gasar da suka hada:
A bangaren haddar dukkanin Alkur'ani:
(1). Mujtaba Fardifani (Iran)
(2). Abdul'aziz Ahmad (Masar)
(3). Muhammad Ali Abdullah (Australiya).
(4). Khalid Sangari (Ivory Coast)
(5). Muhammad Taha Hasan (Nijar)
Sai kuma a bangaren karatun Alkur'anin inda a nan ma:
(1). Hamid Wali Zadeh (Iran)
(2). Muhammad Jawid Akbari (Afghanistan)
(3). Bahruddeen Sa'id (Indonusiya)
(4). Sayyid Abbas Ali (Jamus)
(5). Mustafa Ali (Holland).
Har ila yau kuma sai Raja Ayyoub daga Tanzaniya wanda aka zaba a matsayin makarancin da ya fi sauti da dai sauransu.
Sama da makaranta 130 da suka fito daga sama da kasashe 75 na duniya suka shiga wannan gasa ta Alkur'ani.