Ziyarar Firaministan Kasar Indiya a Kasar Iran
Firaministan Indiya ya bukaci da fadada alaka tsakanin kasar sa da Jumhoriyar musulinci ta Iran musaman ma kan batun da ya shafi tattalin arziki.
A marecen jiya Lahadi ne Firaministan na kasar Indiya Narendra Modi ya sauka a birnin Tehran inda ya samu kyakkyawan tarbe daga mahukuntan kasar ta Iran, jim kadan bayan saukar Sa Mista Modi ya bayyana kyakkyawan fatanta a wannan wannan ziyaza na karfafa alakar dake tsakanin kasashen gami da fadada alaka a bangaren tattalin arzikin kasashen biyu.
Firaministan na India ya tabbatar da cewa Wayewa da al'adu tsakanin Iran da kuma India, ya share fage na bunkasa alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Firaministan na Indiya na tare ne da rakiyar wata babbar tawagar 'yan siyasa, 'yan kasuwa da kuma masana al'adu da ilimi ,inda tun a jiya aka sanya hanun tsananin buranan Tehran da Dehli a bangaren tattalin arziki, zuba hanun jari, kasuwanci, harakar zirga-zirga da kuma fadada hanyoyin matsigar kayan kasuwanci ta hanyar jiragen ruwa, al'adu da kuma bangaren Ilimi.