Iran Na Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya, Inji Hukumar IAEA
Hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta fitar da wani rahoto yau Juma'a wanda ke cewa, Iran na ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita a watan Janairu tare da mayan kasashen duniya duniya.
Wannan dai shi ne rahoto na biyu da hukumar ta AIEA ta fitar tun dai bayan cimma yarjejeniyar dagewa Iran din takunkuman da aka kakaba mata saboda shirin nukiliyar ta na zamen lafiya da aka dade ana takadama a kai.
kuma a dukkan rahotonin da hukumar ta fitar ta yaba da yadda Iran ta mutunta yarjejeniyar, ta takaita shirin nukiliyar ta.
Wannan matsayin a cewar rahoto da hukumar ta fitar a Vienna zai bada damar ci gaba da aiwatar da yejejeniyar, data shafi takaita yawan urenium din da Iran take fitarwa dama bangaren aikin babban injin ta na yankin Arak.
Hukumar ta AIEA ita ce dai keda nauyin sanya ido akan domin tabbatar cewa Iran ta mutunta yerjejeniyar da aka cimma da ita ko kuma A'a, ta yadda tabbatarwa da duniya cewa shirin nukiliyar ta na zamen lafiya ne.
A watan Yuli bara ne mayan kasashen duniya da suka hada da Sin, Amurka, Faransa, Biritaniya, Rusha hadi da kasar Jamus suka cimma yarjejeniya da Iran wace ta tanadi dage mata takunkuman zaluncin da aka kakaba mata na tsawan shekaru.
Saidai duk da cimma wannnan yarjejeniya Iran tana da ci gaba da zargin Amurka da kin baiwa sauren kasahen duniya yin mu'amula da ita yadda ya kamata musamen ta bangaren daya shafi harkokin bankuna na kasa da kasa.