Iran : Ali Larijani Ya Sake Zama Shugaban Majalisa
May 29, 2016 01:24 UTC
'Yan majalisar dokokin Iran sun sake zaben Ali Larijani a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar.
Larijani dai ya samu kuri'u 173, yayain da abokin takara sa Mohammad Reza Aref, ya samu 103 cikin yawan kuri'un da aka kada.
Dan shekaru 57 a duniya, Lirijani ya lashe zaben da gagarimin rinjaye wanda ya kai kashi 61% na kuri'un da aka kada.
'yan majalisar dokoki 281 ne suka kada kuri'a a cikin 290 da majalisar ta kunsa.
Zaben Ali Larijani na zuwa ne mako guda kacal bayan zaben Ayatollah Ahmad Janati a mastayin shugaban majalisar kwararu ta kasar.
Tags