Tsaro, A Matsayin Babbar Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci A Iran
An Bayyan Cewa Tsaro Da Zaman Lafiya Ne Babban Sakamakon Juyin Juya Halin Musulunci.
Wani Kwararre akan harkokin al''adu ya bayyana cewa; Tsaron shi ne babban sakamakon da juyin musulunci ya kawo wa al'ummar Iran.
Hijjatul-Islam, Umid Ramadani wanda ya gabatar da jawabi awurin bikin cikar shekaru 37 da cin nasarar juyin musulunci a jiya laraba da dare a garin Kangawar, ya ce; Duk da kokarin kawo cikas da makiya su ke yi,sai dai a tsawon shekaru 37 na cin nasararsa juyin ya zo wa al'ummar Iran da albarkatu masu yawa.
Umid Ramadhani ya ci gaba da cewa; Idan aka yi la'akari da halin da kasashen makwabta su ke ciki za iya cewa ni'ima mafi girma da juyin ya zo wa al'ummar Iran da ita, ita ce ta tsaro da zaman lafiya.
A yau ne dai al'ummar Iran su ke raya ranar zagayowar cikar shekaru 37 da cin nasarar juyin musuluci a duk fadin kasar. Miliyoyin mutane ne su ka cika titunan birane da kauyuka domin yin tattaki da jerin gwano na girmama wannan rana.