Iran : Rohani Ya Jinjinawa Al'ummar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i616-iran_rohani_ya_jinjinawa_al'ummar_iran
Rohani ya ce al'ummar Iran zasu ci gaba da cimma gurin su, saboda haddin kai da fahimtar juna da suka dashi
(last modified 2018-08-22T06:57:48+00:00 )
Feb 11, 2016 07:20 UTC
  • shugaba Ruhani a tattakin zagayowar shekaru 37 da nasara juyi
    shugaba Ruhani a tattakin zagayowar shekaru 37 da nasara juyi

Rohani ya ce al'ummar Iran zasu ci gaba da cimma gurin su, saboda haddin kai da fahimtar juna da suka dashi

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rohani ya bayanna a yau cewa al'ummar Iran zasu ci gaba da cimma gurin su, saboda haddin kai da fahimtar juna da suka dashi.

Rohani wanda ke bayyana hakan a yayin jawabin sa na zagayowar shekaru 37 da nasara juyun juya halin musulinci a Iran, ya kuma yi godiya ga al'ummar kasar tare da jinjina masu akan juriyar da suka nuna a tsawan wadanan shekaru.

A hannu daya daya tabo batun tsaro shugaba Rohani ya ce, da ikkon Allah batun tsaro saidai a bada misali da Iran a yankin gabas ta Tsakiya, kana kasashen duniya sun zura iddo ga ayyukan Iran yanzu, wanda za'a iya cimma gurin su tare da tallafin al'ummar kasar da biyaya ga umurnin jagoran juyin juya halin musulinci na kasar.

yau ne dai al'ummar Iran ke bikin zagayowar cika shekaru 37 da samun nasara juyin juya halin kasar na ranar 11 ga watan Fabairun shekara 1979 karkashin jagorancin Iman Khomaini