Miliyoyin Iraniyawa Suna Makokin Wafatin Marigayi Imam Khumaini (q) Karo Na 27
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i6181-miliyoyin_iraniyawa_suna_makokin_wafatin_marigayi_imam_khumaini_(q)_karo_na_27
Miliyouin Iraniyawa suna suna gudanar da makokin rasuwar Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jumhuriyar Musulunci ta Iran shekaru 37 da suka gabata.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 03, 2016 00:16 UTC
  • Miliyoyin Iraniyawa Suna Makokin Wafatin Marigayi Imam Khumaini (q) Karo Na 27

Miliyouin Iraniyawa suna suna gudanar da makokin rasuwar Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jumhuriyar Musulunci ta Iran shekaru 37 da suka gabata.

Miliyouin Iraniyawa suna suna gudanar da makokin rasuwar Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jumhuriyar Musulunci ta Iran shekaru 37 da suka gabata.

A nan birnin Tehran ana saran miliyoyin masoyan Imam daga ciki da wajen kasar ne zasu halarci makokin da za'a gudanar a humbarensa mai tsarki a nan kudancin Tehran. Ana saran Jagoran juyin juya halin Musulunci Aya . Sayyeed Aliyul Khaminae zai gabatar da jawabi nan gaba kadan a cikin haraminsa.

An haifi Marigayi Imam Khomani (q) a garin Khumain a nan Tsakiyar kasar Iran ya tashi a gidan malamai, ya kuma fara gwagwarmaya da sarakunan Palawi a kasar ne a shekara 1963, sannan ya yi gudun hijira na tsawon shekaru 15 a kasashen waje, sannan ya dawo a ranar 1-Febrerun-1979 inda ja kammala jagorancin juyin juya halin zuwa ga nasara. Ya kuma jagoranceta na tsawon shekarum 10 sannan ya rasu yana dan shekara 87 a duniya a ranar 3-Jyuin-1989M.