Lokacin kakabawa Al'ummar Iran ya Kawo karshe
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i619-lokacin_kakabawa_al'ummar_iran_ya_kawo_karshe
Shugaban jumhoriyar musulinci na Iran ya bayyana cewa Lokacin kakkaba takunkumi da kuma kaskantar da Al'ummar Iran ya kawo karshe.
(last modified 2018-08-22T06:57:48+00:00 )
Feb 11, 2016 11:10 UTC
  • Lokacin kakabawa Al'ummar Iran ya Kawo karshe

Shugaban jumhoriyar musulinci na Iran ya bayyana cewa Lokacin kakkaba takunkumi da kuma kaskantar da Al'ummar Iran ya kawo karshe.

Shugaba Rauhani ya bayyana haka ne a yayin da yake halartar taron bikin zagayowar ranar juyin juya halin musulinci na kasar da ya gudana safiyar yau a babban dandalin Azadi dake nan birnin Tehran, inda ya ce Duniya ta fahimce cewa wajibi ne a tattauna da Al'ummar Iran cikin yaran kirmamawa da karamci.

Dr Hasan Rauhani ya kara da cewa lokacin ci gaban kasar da kokarin Al'umma ya zo, domin haka wajibi ne dukkanin 'yan kasa su yi hubbasa domin gina kasar Su da kuma cimmata gaba.

shugaba Rauhani ya tabbatar da cewa juyin juya halin musulinci ba na wani gungun siyasa ba ne, musulinci, kyawawen dabi'u da kuma hadin kai Al'umma shine abin da juyin juya halin musulinci ya gadar, domin haka wannan bai kebanta ga wani gungun siyasa ba, juyi ne na Al'ummar Iran da kuma dukkanin masu neman 'yanci na Duniya baki daya.

A nasa bangare, shugaban hukumar tsaron kolin kasar ya tabbatar da cewa Al'ummar kasar Iran, Al'umma ce dake son sulhu da konciyar hankali wacce take iya kokarinta wajen tabbatar da tsaro da sulhu a yankin da Duniya baki daya, kuma Gwamnati da taimakon Al'umma tareda shiryarwa jagora juyin juya halin musulinci sun samu nasarar dakille duk wani kokarin makiya.