Bunkasar Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Iran Da Malaysia
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i6385-bunkasar_alakar_tattalin_arziki_da_cinikayya_tsakanin_iran_da_malaysia
Jakadiyar kasar Iran a kasar Malaysia ta bayyana gagarumin ci gaban da aka samu a tsakanin Iran da Malaysia ta fuskar harkokin tattalin arziki da cinikayya.
(last modified 2018-08-22T06:58:24+00:00 )
Jun 07, 2016 11:42 UTC
  • Bunkasar Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Iran Da Malaysia

Jakadiyar kasar Iran a kasar Malaysia ta bayyana gagarumin ci gaban da aka samu a tsakanin Iran da Malaysia ta fuskar harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Kmafanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, a yau jakadiyyar kasar Iran a Malaysia Mardiya Afkham ta gana da shugaban majalisar dattijan kasar ta Malaysia a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, inda suka tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban majalisar dattijan kasar Malaysia S. Vigneswaran ya bayyana alaka a tsakanin kasarsa da Iran da cewa, alaka ce ta tarihi, kuma tana samun ci gaba a wanann lokaci fiye da kowane lokaci, musamamn ta fuskar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu.