Barka Da Salla
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya yi wa Kasashen Musulmi Barka da Salla.
shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran, Dr. Ali Larijani, ya aike da sakon barka da salla ga takwarorinsa na kasashen musulmi.
Gidan Radiyo ta telbijin na Iran na ambato majiyar majalisar shawarar musulunci tana cewa sakon da Larijani ya aike ya kunshi bayyana idi a matsayin wata rahama daga Ubangiji da kuma neman samun gafara daga Ubangiji madaukakin sarki.
Har ila yau, sakon na Dr. Ali Larijani ya yi fatan ganin cewa azumin wata guda na Ramadhan da musulmin su ka yi, ya zamar musu wata dama ta bunkasa rayuwarsu, da kuma kawar da duk wani sabani a tsakaninsu.
A yau talata ne wasu kasashen na musulmi su ke yin salla, yayin da wasu sai gobe laraba.