Tehran: Hudubar Sallar Juma'a
(last modified Fri, 08 Jul 2016 19:03:02 GMT )
Jul 08, 2016 19:03 UTC
  • Tehran: Hudubar Sallar Juma'a

Limamin Tehran Ya Bayyana Amurka A matsayin ummul-haba'isin rashin tsaro a duniya.

Wanda ya jagoranci sallar juma'a a yau, anan birnin Tehran, ya bayyana cewa; Yake-yake da rashin tsaro a duniya sun samo tushe ne daga kasashe masu girman kai a duniya, musamman ma dai Amurka.

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidy Karmany, ya ce; kasashe masu takama da karfi a duniya, suna son a shigar da batun Palasdinu cikin kwandon shara, amma kuma alokaci guda su ne su ke bada taimako ga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Limamin na Tehran ya kara da cewa; Kasashe masu girman kai sun maida sabanin da ake da shi a cikin kasashen wannan yankin ya zama yaki, sannan kuma su ke daga taken fada da ta'addanci.

Har ila yau, Ayatullahi Muwahhidy Karmany ya ce; Dalilan da su ka sa kasashen turai su ke haddasa yake-yake shi ne samun damar wawason albarkatun man fetur din da su ke cikin kasashen.