Iran Ta Kirayi Jakadan Faransa Game da Taron MunafikanTa A Paris
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i8074-iran_ta_kirayi_jakadan_faransa_game_da_taron_munafikanta_a_paris
Iran ta ja kunnan Faransa game da wani taro da manufikan ta dake ketare suka gudanar a Paris a ranar 9 ga watan nan.
(last modified 2018-08-22T11:28:35+00:00 )
Jul 13, 2016 11:06 UTC
  • Iran Ta Kirayi Jakadan Faransa Game da Taron MunafikanTa A Paris

Iran ta ja kunnan Faransa game da wani taro da manufikan ta dake ketare suka gudanar a Paris a ranar 9 ga watan nan.

Iran ta nuna matukar bacin ran ta dangane da taron da tace na makiyan ta ne da azulumai da suka cuci al'ummar kasar, wanda ta danganat da mafi muni da 'yan taliban ko kuma Al'Qaida ko (IS).

A cikin wasikar data mikawa jakadan na faransa da yammacin jiya Iran ta ce ba zata taba amuncewa da irin wannan taro na bata sunan kasar da firta kalamai marasa dadi ga kasar a cikin kasar ta faransa.

hakazalika Iran ta ce zata ci gaba da yakar wadanan manafikan kuma tana allawadai da duk wata gwamnati dake goyan bayansu ta kasance ta Turai ko kuma a yankin.