Iran Ta Bukaci Amurka Ta Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya
Jul 15, 2016 09:35 UTC
Ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya yi kira ga Amurka da ta mutunta yarjejeniyar nukiliyar a aka cimma da kasar sa shekara guda bayan cimma yarjejeniyar da mayan kasashen duniya.
Yarjejeniyar data soma aiki a watan Janairu ta bada damar dagewa Iran wani bangare na takunkuman kada da kasa da aka kakaba mata, da nufin takaita shirin nukiliyar ta.
Saidai Iran na allawadai da yadda har yanzu Amurka ke jan kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar musamen ta bangaren harkokin kudi, kamar yadda Mr Zarif ya bayana a shafinsa na Twitter.
A nata bangare Amurka ta bakin sakataren harkokin kudin ta, Jacob Lew ta musunta cewa bata niyyar aiwatar da yarjejeniyar.
Tags