Ziyarar Shugaba Rauhani A Yankin Kurdawa Na Kermanshah Da Ke Yammacin Iran
A yau ne shugaba Rauhani na kasar Iran ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yankin Kermanshah na kabilar Kurdawa da ke yammacin kasar.
A yayin ziyarar tasa a yau, shugaba Rauhani ya samu tarba daga dubban daruruwan Kurdawa mazauna wanann yanki.
A jawabin da ya gabatar a gaban dubun-dubatar jama'a da suka taru, shugaba Rauhani ya jinjina wa al'ummar wannan yanki dangane da sadaukarwar da suka yi ga juyin juya halin muslunci na Iran, tare da bayyana su a matsayin abin buga misali.
Al'ummar yankin Kermanshah dai Kurdawa ne mabiya mazhabobi na sunnah da suke rayuwa a kasar Iran, wadanda suke da wakilci a majlisar dokoki da sauran dukkanin bangarori na gwamnatin kasar Iran, kamar yadda kuma suke rike da mukamai da suka hada da ministoci da manyan daraktoci a ma'aikatun kasar.