Zarif: Amurka Ce A Baya Baya Wajen Aiwatar Da Alkawulan Yerjejeniyar Nuklia
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i8320-zarif_amurka_ce_a_baya_baya_wajen_aiwatar_da_alkawulan_yerjejeniyar_nuklia
Amurka ce a baya wajen aiwatar da yerjejeniyar nuklia ta kulla da Iran a bara
(last modified 2018-08-22T06:58:37+00:00 )
Jul 18, 2016 13:28 UTC
  • Zarif: Amurka Ce A Baya Baya Wajen Aiwatar Da Alkawulan Yerjejeniyar Nuklia

Amurka ce a baya wajen aiwatar da yerjejeniyar nuklia ta kulla da Iran a bara

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya ce gwamnatin kasar Amurka ce a baya baya wajen cika alkawulan da ta cimma da Iran a yerjejeniyarta da kasashen 5+1 kan shirinta makamshin nuklia a shekara da ta gabata.

Zarif ya bayyana haka ne a jiya a lokacinda yake hira ta musamman da tashar television ta IRIB NEWS a dai dai lokacinda yerjejeniyan take cika shekara guda da fara aiwatarwa.

A ranar 14-Yuli-2015 ne kasar Iran ta cimma yerjejeniyar da manya manyan kasashen duniya 5 masu kujerun din din din a komitin tsaro na majalisar dinkin duniya hada da kasar Jamus, kan shirin ta na makamshin nuklia. Yerjejeniyar ta bukaci a daukewa iran dukkan takunkuman da aka dora mata kan shirinta na makamashin nuklia, wadanda suka hada da na tarayyar Turai, Majalisar dinkin duniya da kuma ita Amurka, a yayinda ita kuma a nata bangaren zata takaita shirinta na makamashin nuklia zuwa wasu shekaru masu zuwa.

Zarif ya ce yerjejeniyar da ake kira "the Joint Comprehensive Plan of Action" (JCPOA) , babban nasara ce ga Jumhuriyar musulunci ta Iran, don ko ba kome ta tabbatar da gaskiyar kasae Iran a shirin nata, sannan an dauke mata dukkan takunkuman da aka doramat a wannan bangaren. Sai dai akwai wasu bankuna a wasu kasashen turai da Amurka wadanda suke dari dari kan budewa iran kofofinsu don tsoron gwamnatin kasar ta Amurka har yanzu.