Hudubar sallar Juma'a A Yau A Tehran
(last modified Fri, 22 Jul 2016 16:51:18 GMT )
Jul 22, 2016 16:51 UTC

Wanda ya jagorancin sallar Juma'a a Juma'a a yau a Tehran ya yi kakkausar suka dangane da zaluncin da al'ummar Bahrain suke fuskanta daga masarautar mulkin kama karya ta kasar.

A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a  yau Tehran, Ayatollah Ahmad Khatami ya bayyana masu mulkin kasar Bahrain a matsayin wadanda ba su da ikon kasar a hannunsu sai abin da Amurka ta ga dama shi ne suke aiwatarwa, ko da hakan kuwa zai jawo fitina  atsakaninsu da al'ummar kasar.

Malamin ya yi ishara da abin da ya faru na janye izinin zama dan kasa daga kan Ayatollah Isa babban malamin kasar wanda ke da asali mai tushe a kasar tun kaka da kakakin, wanda hakan ke nuni da cewa wanann mataki ya fi gaban mahukuntan kasar, Ayatollah Khatami ya gargadi sarakunan Bahrain da su shiga taitayinsu dangane da duk wani abin da ka iya samun Ayatollah Isa Kasim, matukar dai suna son zaman lafiya a kasar.

Haka nan kuma malamin ya bayyana abin da ya faru a kasar Turkiya a lokacin yunkurin juyin mulki da cewa ba abu ne mai faranta rai ba, domin kuwa duk abin da zai kai ga zubar da jinin dan adam fitina ne a bayan kasa, tare da yin fatan a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Kamar yadda kuma ya soki lamirin wasu daga cikin kasashen larabawa dangane da halin ko in kula da suke nunwa kan kisan kiyashin da Isra'ila take yiwa Palastinawa a kowace rana ta Allah, a maimakon kare Palastinawan ma,a  halin yanzu manyan kasashen larabawa suna kokarin shelanta alakarsu a fili tare da Isra'ila, bayan alakarsu ta bayan fage, wanda hakan ke nufin bayar da lasisi ga Isra'ila kan ta ci gaba da cin karenta babau babbak a kan al'ummar musulmin Palastinu.

A daya bangaren kuma Ayatollah Khatami ya tabo batun harin da aka kai a kasar Faransa, wanda musulmi 30 daga cikin mutane 84 suka rasa rayukansu, inda ya ce hakan ya kara tabbatar wa duniya cewa abin da 'yan ta'adda suke yi ba shi ne musulunci ko kuma sunanr manzon Allah da suke raya cewa suna bi ba, domin kuwa hatta sauran musulmi da ba a cikinsu suke ba, ba su tsira daga sharrinsu ba.