Iran Da Tarayyar Turai Sun Tattauna Kan Bunkasa Tattalin Arzikinsu
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i8968-iran_da_tarayyar_turai_sun_tattauna_kan_bunkasa_tattalin_arzikinsu
Wata tawagar kungiyar tarayyar turai ta iso birnin Tehran a yammacin jiya Lahadi, domin tattaunawa tare da manyan jami'an gwqamnatin Iran kan hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu, da kuma batun ayyukan fito.
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Aug 01, 2016 01:23 UTC
  • Iran Da Tarayyar Turai Sun Tattauna Kan Bunkasa Tattalin Arzikinsu

Wata tawagar kungiyar tarayyar turai ta iso birnin Tehran a yammacin jiya Lahadi, domin tattaunawa tare da manyan jami'an gwqamnatin Iran kan hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu, da kuma batun ayyukan fito.

Tawagar kungiyar tarayyar turan karkashin jagorancin Errec Mammer, ta iso birnin Tehran a yammacin Lahadi, tawagar dai ta kunshi manyan jami'ai na kungiyar tarayyar turai a bangaren harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Tun a daren jiya ne aka fara gudanar da zama a tsakanin bangarorin biyu, domin samun daidaito kan batutuwan da suka danganci bunkasa harkokin tattalin arziki tsakanin tarayyar turai da kuma Iran, da hakan yaha da harkokin banki, da kuma yadda za a rika fitar da kaya daga bangarorin biyu.