A gobe alhamis, Rasha Za ta aikowa da Iran Makamin s300
Feb 17, 2016 09:07 UTC
A gobe alhamis ne za a aiko da makamin S300 na kakkabo jiragen yaki, zuwa Iran ta hanyar tekun Caspian.
Kamfanin Dillancin Labarun Spotnik na kasar Rasha ya ce Ministan tsaron Iran Hussain Dahqan wanda yanzu haka ya ke ziyara a kasar Rasha, zai halarci gabar ruwan garin Astarakhan,da za a aiko da makaman.
Shi dai makamin S300 za a yi amfani da shi ne a Iran domin kare masana'antu da cibiyoyin gwmanati da sansanoni soja. Makamin zai iya kakkabo jiragen yaki da kuma makamai masu linzami samfurin Ballastic.
Dauke takunkumin da aka kakabawa Iran ne dai ya bada damar bata makamin wanda aka kulla yaejejniya akansa tun a shekarun baya.
Tags