Ayatullahi Kermani :Mumunar Siyasar Saudiya ya yi babbar illa ga Musulmin Duniya
Wanda ya Jagoranci Sallar Juma'a na birnin Tehran ya ce rashin iya siyasa na magabatan Saudiya musaman ma kan aiyukan Hajji yayi sanadiyar illa ga Al'ummar musulmin Duniya.
A yayin da yake ishara kan sharudan da aka gindayawa Jumhoriyar musulinci ta Iran da hakan ya hana Alhazantan ta zuwa aikin hajjin bana, Limamin da ya jagorancin Sallar Juma'a na nan birnin Tehran, Ayatul...muhamad Ali Muwahidi Kermani ya tabbatar da cewa mahukuntan Saudiyan na kiran kansu masu bin Alkur'ani da sunna, amma aiyukan su ya sabawa musulinci kuma duk wani abu da su ke yi a halin da ake ciki ba maslahar Al'ummar musulmi ba ne.
Ayatull..Kermani ya ce mu'amalar da mahukuntan Saudiya ke yi babu abinda yake janyo musu face gyama da kuma kara tsana daga Al'ummar musulmin Duniya,kuma idan suka ci gaba da wannan siyasa za su kasance cikin tsoro da fargaba ko da a yayin da su shiga cikin masallaci mai alfarma ne.
Limamin ya kara da cewa bisa Umarnin Alkur'ani mai girma duk wanda ya hana Al'ummar musulmi zuwa aikin Hajji zai hadu da Azaba mai radadi.
A yayin da ya koma kan rikicin yankin gabas ta tsakiya musaman ma rikicin kasashen Yemen da Siriya, Ayatul...muhamad Ali muwahidi Kermani ya bayyana kyakkyawan fatan sa ga Al'ummar wadannan kasashe, inda ya ce Al'ummar wadannan kasashen sun nuna juriya wajen yaki da ta'addancin kasar Amurka, Haramcecciyar kasar Isra'ila gami da mahukuntar saudiya, kuma muna kyautata fatan cewa nan ba da jumawa ba za su ci nasara, tsaro da konciyar hankali ya dawo cikin kasashen su.