Salihi : Juyin Islama Shi Ne Babbar Matsalar Yammacin Turai Da Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9385-salihi_juyin_islama_shi_ne_babbar_matsalar_yammacin_turai_da_iran
Shugaban hukumar makamashin nukilya ta kasar Iran Dr. Ali Akbar Salhi ya bayyana cewa, kasashen yammacin turai ba su da wata matsala da shirin Iran na nukiliya, ko tattalin arziki Iran, ko bunkasar ci gabanta a bangaren ilimin kimiyya da fasaha, babbar matsalarsu da Iran ita ce juyin juya halin muslunci.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 09, 2016 17:11 UTC
  • Salihi : Juyin Islama Shi Ne Babbar Matsalar Yammacin Turai Da Iran

Shugaban hukumar makamashin nukilya ta kasar Iran Dr. Ali Akbar Salhi ya bayyana cewa, kasashen yammacin turai ba su da wata matsala da shirin Iran na nukiliya, ko tattalin arziki Iran, ko bunkasar ci gabanta a bangaren ilimin kimiyya da fasaha, babbar matsalarsu da Iran ita ce juyin juya halin muslunci.

Salihi ya bayyana hakan ne a yau a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taron masana a birnin Tehran, inda ya ce babbar matsalar kasashen yamamcin turai ita ce juyin juya halin da ya baiwa Iran damar zama kasa mai 'yancin siyasa, wanda kuma dukkanin ci gabanta a bangaren nukiliya da ilimin kimiyya da fasaha da sauransu, sakamako ne na 'yancin siyasa da take da shi, domin hakan ne ya sanya ba ta dogara da su ba, sabanin sauran kasashen duniya da suka dogara da su.

Daga karshe Salihi ya ce yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da kasashen duniya tana nan kamar aka rubuta ta, kuma Iran tana yin aiki da ita kamar yadda aka cimmawa tsakaninta da sauran kasashe, amma rashin yin aiki da ita daga wani bangare, hakan zai sanya Iran ta yi watsi da ita baki daya.