Saudiya ta hana 'yan kasar Iran mazauna kasashen Turai biza
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9481-saudiya_ta_hana_'yan_kasar_iran_mazauna_kasashen_turai_biza
Kasar Saudiya ta ki bawa yan kasar Iran mazauna kasashen Turai biza
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 11, 2016 14:29 UTC
  • Saudiya ta hana 'yan kasar Iran mazauna kasashen Turai biza

Kasar Saudiya ta ki bawa yan kasar Iran mazauna kasashen Turai biza

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya nakalto Husaini Tahmasi shugaban masu  jagorantar tawagar mazauna Iran a birnin London zuwa aikin hajji ya ce har ya zuwa yanzu Gwamnatin Saudiya ba ta basu bisa na zuwa aikin hajjin bana ba.

Shugaban tawagar 'yan kasar Iran mazauna kasashen Turai ya ce magabatan Saudiyan sun yi watsi da takardun daya daga cikin jagoran tawagar maniyata aikin hajji 'yan kasar iran din dake nan kasar Burtaniya saboda laifin ya yi hira da 'yan jaridu bayan turmutsitsin mahajjata a Mina shekarar da ta gabata.

Tahmsani ya kara da cewa magabatan Saudiya na kokarin bin wasu hanyoyi kamar yin barazana da sauransu ga shugabanin tawagar Alhazan kasashen musulmi na ganin cewa kadda su sake su fadi wani laifi na magabatan Saudiya.

A shekarar da ta gabata Dubun dubatan musulmi ne suka rasa rayukansu A Mina sanadiyar turmutstsi da ya faru, daga cikin su a kwai 'yan kasar 464.