Iran Ta Sake Samon Wata Nasara Kan HKI A Kotu
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9514-iran_ta_sake_samon_wata_nasara_kan_hki_a_kotu
Iran ta sake samun nasara kan HKI a wata kotu koli a kasar Switzerland
(last modified 2018-08-22T11:28:45+00:00 )
Aug 12, 2016 08:25 UTC
  • Iran Ta Sake Samon Wata Nasara Kan HKI A Kotu

Iran ta sake samun nasara kan HKI a wata kotu koli a kasar Switzerland

Wata babbar kotun kasa da  kasa a kasar Swirzerland ta yi watsi da daukaka karan da HKI ta yi a kan biyan kasar Iran kudaden da take binta a wata yerjejeniyar shimfida bututun mai da suka kulla kafin nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979. Gwamnatin sarki Mohammad Reza Pahalawi ta kulla yerjejeniya da kamfanin HKI na Eilat-Ashkelon Pipeline Co. (EAPC a shekara 1968 na shimfida bututun mai wanda zai kai danyen man kasar Iran zuwa bakin tekun Medeteranian amma sanadiyyar nasarar juyinn juya halin musulunci a kasar kamfanin yahudawan ya dakatar da aikin ya ki kuma biyan kasar Iran kudaden da ya karba. A halin yanzu dai dole HKI ta biya Iran dalar Amurka billion 1.1 da kuma karin kudin ruwa na dalar Amurka dubu 461,000.

Kafin haka a farkon wannan watan ne wata kotun koli a kasar Switzerlanda ta yi watsi da daukaka karar da HKI ta yi kan hukuncin da  wata karamar koto ta yanke na biyan kasar Iran dalar Amurka billion 1.2 kudaden man fetur da kasar Iran ta sayarwa HKI kafin nasara juyin juya halin musulunci kasar amma bata biya ba. A halin yanzu dai kasar Iran tana bin HKI jimillan kudaden da suka kai dalar Amurka billion7.