Zarif Zai Ziyarci Wasu Kasashen Latine Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9808-zarif_zai_ziyarci_wasu_kasashen_latine_amurka
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Javad Zarif zai fara wani ran gadi a wasu kasashen Latine Amurka guda shida a wannan Lahadin.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Aug 18, 2016 11:11 UTC
  • Zarif Zai Ziyarci Wasu Kasashen Latine Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Javad Zarif zai fara wani ran gadi a wasu kasashen Latine Amurka guda shida a wannan Lahadin.

Wannan ziyara ta Mr Zarif nada nufin karfafa alaka da kasashen ta fuskar siyasa da kuma tattalin arziki.

Mr Zarif ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter a harshen turancin Ingila da kuma Spaniya.

koda yake bayanin bai zayyano kasahen da Mr Zarif zai ziyarta ba kawo yanzu, amma dai zai kasance tare da rakiyar wata babbar tawaga ta 'yan kasuwa da masu zuba jari na kasar ta Iran.