Hudubar Sallar Juma'a A Babban Masallacin Birnin Tehran Na Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9862-hudubar_sallar_juma'a_a_babban_masallacin_birnin_tehran_na_kasar_iran
Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa yana daga cikin sabon makircin manyan kasashen duniya masu girman kai da yahudawan sahayoniyya sake farfado da kungiyar ta'addanci ta munafukai da suke fada da tsarin Musulunci a kasar Iran.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 19, 2016 12:30 UTC
  • Hudubar Sallar Juma'a A Babban Masallacin Birnin Tehran Na Kasar Iran

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa yana daga cikin sabon makircin manyan kasashen duniya masu girman kai da yahudawan sahayoniyya sake farfado da kungiyar ta'addanci ta munafukai da suke fada da tsarin Musulunci a kasar Iran.

A hudubar sallar Juma'arsa a babban Masallacin Juma'ar birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau: Ayatullahi Ahmad Khatami ya tabo bakar siyasar Amurka da mahukuntan Saudiyya na kokarin sake farfado da kungiyar ta'addanci ta munafukai da suke adawa da tsarin Musulunci a kasar Iran {Mujahidin Khaliq} tare da ware miliyoyin kudade na dalar Amurka;Yana mai fayyace cewa: Manufar wannan bakar siyasa ita ce yin amfani da kungiyar ta'addancin ta munafukai a kan al'ummar yankin gabas ta tsakiya ciki har da kasar Iran kuma mahukuntan Saudiyya sun dauki alhakin wadata kungiyar da kudade da makamai.

Ayataullahi Khatami ya jaddada cewa: A fili yake cewa kungiyar ta'addanci ta munafukai ta riga ta rushe kuma duk wani kokari da manyan kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka da 'yan koranta na yankin gabas ta tsakiya zasu yi na sake farfado da kungiyar ba zai kai ga samun nasara ba.

Ayatullahi Khatami ya kuma tsakuro wani abu daga cikin ayyukan ta'addancin kungiyar munafukai ta Mujahidin Khaliq na kashe-kashen gilla da suka kai ga shahadan mutane kimanin 17,000 a sassa daban daban na kasar Iran.