An kame wasu 'yan ta'adda a yammacin Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9916-an_kame_wasu_'yan_ta'adda_a_yammacin_iran
Ma'aikatar tattara bayanan sirri ta kasar Iran da sanar da kame wata tawagar 'yan ta'adda a yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:47+00:00 )
Aug 21, 2016 05:46 UTC
  • An kame wasu 'yan ta'adda a yammacin Iran

Ma'aikatar tattara bayanan sirri ta kasar Iran da sanar da kame wata tawagar 'yan ta'adda a yammacin kasar.

Kamafanin dillancin Labaran Irna na kasar Iran ya Habarta cewa Ma'aikatar tattara bayanan sirri ta kasar ta sanar da cewa bayan fatattakar da jami'an tsaro suka yiwa 'yan ta'adda masu akidar kafirta musulmi a ranaikun 15 da 16 a wannan wata na Agusta da muke ciki, Jami'an tsaron sun ci gaba da farautar sauran 'yan ta'addar inda a ranar 18 ga wannan wata da muke ciki aka gano maboyar su tare kuma da kame babbar tawagarta su.

Sanarwa ta kara da cewa rundunar hadin gwiwar ta Dakarun juyin juya halin musulnci sun samu nasarar gano maboyar 'yan ta'addar sannan kuma sun kame makamai , gurneti, ababen fashewa, Na'urorin aikin soja, ababen da ake hada bama-bamai gami da sauren kayan aikin ta'addanci a tare da 'yan ta'addar.