Iran Da Rasha Suna Da Kusancin Fahimta Wajen Fada Da Ta'addanci
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran: Iran Da Rasha Da Kusancin Mahanga Kan Fada Da Ta'addanci.
Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya ce; Matsayar Iran akan fada da ta'addanci ta yi kusa da ta kasar Rasha.
Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran Bahram Qasimy wanda ya ke gabatar da taron manema labaru na mako-mako a yau litinin ya yi ishara da batun amfani da filin saukar jirajen yaki na Hamadan da kasar Rasha ta ke yi inda ya ce; " Babu wata rubutacciyar yarjejeniya a tsakanin Iran da Rasha kan batun, sai dai da akwai bangarori da dama da aka samu ci gaba na azo a gani a tsakanin kasashen biyu.
Dangane da rade-radin ziyarar da shugaban kasar Turkiya zai kawo Iran kuwa, kakakin ma'aikatar ma'akatar harkokin wajen na Iran ya ce; Alaka a tsakanin Iran da makwabciyarta Turkiya tana da kyau, kuma Iran ce kasar farko da ta fara maida martani bayan juyin mulkin da bai kai ga yin nasara ba.