Iraki: An Rataye 'Yan Ta'adda 36 Kan Kisan Mutane 1700
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10024-iraki_an_rataye_'yan_ta'adda_36_kan_kisan_mutane_1700
A ranar Lahadi 21 ga wata Agusta 2016, ma'aikatar shari'a a kasar Iraki ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan mutane 36, wadanda suke da hannu a kisan gillar da aka yi wa daliban makarantar soji ta Sabaikar su 1700 a cikin watan Yulin shekara ta 2014, a lokacin da 'yan ta'addan ISIS suka shiga cikin lardin Salahuddin.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Aug 23, 2016 00:53 UTC
  • Iraki: An Rataye 'Yan Ta'adda 36 Kan Kisan Mutane 1700

A ranar Lahadi 21 ga wata Agusta 2016, ma'aikatar shari'a a kasar Iraki ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan mutane 36, wadanda suke da hannu a kisan gillar da aka yi wa daliban makarantar soji ta Sabaikar su 1700 a cikin watan Yulin shekara ta 2014, a lokacin da 'yan ta'addan ISIS suka shiga cikin lardin Salahuddin.

An zartar da wanan hukunci ne a kan mutanen bayan kwashe tsawon lokaci ana shari'a tare da gudanar da bincike kan lamarin, inda bayan tabbatar da hannunsu a cikin wannan danyen aiki, an zartar da hukuncin kisa a kansu a cikin gidan kaso na birnin Nasiriyyah da ke cikin lardin Ziqar, tare da halartar ministan shari'a na kasar Iraki da kuma iyalan wasu daga cikin wadanda 'yan ta'addan suka yi wa kisan gilla.

Zartar da wannan hukunci dai ya samu karbuwa tare da faranta rayukan  al'ummar kasar Iraki, musamman ma al'ummar birnin Nasiriyya da aka zartar da wannan hukunci a cikinsa, kasantuwar cewa fiye da mutane 400 daga cikin mutane 1700 da 'yan ta'adda suka yi wa kisan gilla sun fito daga birnin na Nasiriyya ne.

'Yan ta'addan ISIS sun aiwatar da wannan mummunan aiki ne tare da hadin baki da wasu daga cikin gwamnatocin kasashen larabawa da suke daukar nauyinsu tare da taima musu wajen mamaye wasu daga cikin yankunan kasar Iraki a cikin shekara ta 2014, da nufin rusa kasar kamar yadda suka yi a Syria, inda da dama daga cikin 'yan ta'addan wadanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen duniya ne daban-daban musamman na larabawa, suke raya cewa suna yin jihadi ne domin kafa abin da suke kira daular muslunci.

Ko shakka babu daukar wannan mataki na zartar da hukuncin kisa kan 'yan ta'adda a Iraki bai zo wa kowa da mamaki ba, yayin da wasu ma suke ganin an Makara matuka wajen fara aiwatar da wannan hukunci a kan 'yan ta'addan da suke da hannu a kisan gillar Sabaikar, domin kuwa shi ne kisan gilla mafi muni da kungiyar ta fara aiwatarwa a kasar Iraki tun bayan da ta kwace iko da wasu yankunan kasar, inda suka kashe daliban makarantar sojojin su 1700 saboda su mabiya mazhabar shi'a ne, wasu an kashe su ta hanyar harbi da bindiga, yayin da kuma wasu aka kashe su ta hanyar jefa su a cikin ruwa, wasu daruruwa kuma an kashe su ne ta hanyar tona manyan ramuka tare da bizne su da ransu.

Tsarkake birnin Falluja daya daga cikin mayan sansanoni da 'yan ta'addan ISIS suka yi dandazoa  cikinsu a kasar ta Iraki da aka yi a kwanaki baya, na daya daga cikin abubuwan da suka kara wa rundunar sojin kasar Iraki karfin gwiwa wajen kafa zage dantse a yakin da suke yi da 'yan ta'addan takfiriyyah Wahabiyyah na ISIS, musamman ganin cewa sun kwace birnin na Falluja ne da kansu ba tare da neman taimako daga wata kasa ba, wanda kuma ko shakka babu hakan ya yi tasiri ta hanyar saka tsoro a cikin zukatan 'yan ta'addan, da kuma kaduwa ga  kasashen da suke daukar nauyinsu, domin kuwa a lokacin ministan harkokin wajen masarautar Saudiyya da yake ziyarar aiki a birnin Brussels na kasar Belgium, a zantawarsa da manema labarai ya yi Allawadai da kakkausar murya, kan abin da ya kira yunkurin da  sojojin gwamnatin Iraki suke yi na kwace iko da birnin Falluja daga hannun kungiyar ISIS, inda ya ce dakarun na Iraki suna yaki ne da 'yan Sunnah a Falluja, furucin da dama daga cikin masana siyasa na kasa da kasa suka bayyana shi da cewa, alama ce ta rauni da kuma yanke kauna.