Turkiyya : TAK Ta Dauki Nauyin Kai Harin Ankara
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1006-turkiyya_tak_ta_dauki_nauyin_kai_harin_ankara
Harin na ranar 17 ga watan nan yayi sanadin mutuwar mutane 28 a Ankara
(last modified 2018-08-22T11:27:50+00:00 )
Feb 19, 2016 17:36 UTC
  • Turkiyya : TAK Ta Dauki Nauyin Kai Harin Ankara

Harin na ranar 17 ga watan nan yayi sanadin mutuwar mutane 28 a Ankara

Wani gungun dake dasawa da kungiyar ma'aikatan kurdawa na PKK, mai suna TAK ya dauki alhakin kai harin birnin Ankara na kasar Turkiyya.

Gungun wanda ko a baya ya dau alhakin kai wani harin roka kan filin sauka da tashin jiragen Stanbul, ya kuma dai dau nauyin wannan harin a wani shafin internet.

Harin wanda aka kai da yammacin ranar Laraba data gabata kan wani ayarin motocin sojin kasar a Ankara yayi sanadin mutuwar mutane 28 tare da raunana wani adadi mai yawa.

tunda farko dai shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi alkawarin daukar fansa kan wadanda suka kai harin wanda ya kashe mutane 28 tare da jikkata 61.