Kasar Masar Ta Kafa Sharuddan Maida Alaka Da Turkiya
Aug 24, 2016 07:51 UTC
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ya ce; Da akwai sharudda domin mayar da alaka da Turkiya
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ya ce; Da akwai sharudda domin mayar da alaka da Turkiya
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin Wajen kasar ta Masar Ahmad Abu Zaid, ya ce; Masar tana maraba da duk wani yunkuri na gaskiya da Turkiya za ta nuna domin mayar da alaka a tsakaninsu.
Ahmad Abu Zaid ya kara da cewa; Kyautata alaka a tsakanin kasashen Masar da Turkiya za ta amfani dukkanin kasashen biyu.
Alaka dai a tsakanin Masar da Turkiya ta yi kamari tun bayan kifar da gwamnatin Muhammadu Mursi da Tukiyan ta ke goyawa baya.
Tags