An Kashe Sojojin Saudiyya 8 A Kudancin Kasar
Mayakan Yamen Sun Kashe Sojojin Saudiyya 8
Sojojin Kasar Yamen da mayakan Huthy sun kashe sojojin Saudiyya takwas.
Rahotanni daga kasar Yamen na nuni da cewa; Mayakan kasar ta Yamen da su ka kutsa cikin kasar Saudiyya akan tuddan 'al-shaibany' da ke gundumar al-Asir sun kashe sojojin na Saudiyya bayan da su ka kame yankin.
Bugu da kari, mayakan na Yamen sun rusa motocin yaki da dama da su ke a cikin sansanonin sojojin Saudiyya da su ke akan iyaka.
Kasar Saudiyya tare da wasu kasashen larabawan yankin tekun pasha, bisa jagorancin Amurka, sun shelanta yaki akan al'ummar Yamen fiye da shekara daya da ta gushe.
Kawo ya zuwa yanzu dai dubban mutane ne su ka kwanta dama, yayin da wasu kuma su ka jikkata.