Ci gaban Hare-haren Saudiyya A Kasar Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10408-ci_gaban_hare_haren_saudiyya_a_kasar_yamen
Jiragen Yakin Saudiyya Suna Ci gaba da kai hari a cikin kasar Yamen
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 31, 2016 14:32 UTC
  • Ci gaban Hare-haren Saudiyya A Kasar Yamen

Jiragen Yakin Saudiyya Suna Ci gaba da kai hari a cikin kasar Yamen

A yau laraba Jiragen Yakin kawancen da Saudiyya ta ke jagoranta sun kai hare-hare a yankunan daban-daban na kasar Yamen.

Yankunan da hare-haren na saudiyya su ka shafa sun hada da babban birnin kasar ta Yamen, San'aa da Hajjah da Shibwah da Sa'adah. Fararen huda da dama ne dai su ka kwanta dama da kuma jikkata sanadiyyar hare-haren.

A jiya talata ma dai jiragen yakin na Saudiyya su kashe mutane 16 fararen hulale a harin da su ka kai wa yankin Sa'adah.

A gefe daya, sojojin kasar ta Yamen sun maida martani da harba makami mai linzami a cibiyar masana'antu ta garin Najran da ke kudancin saudiyya, wanda ya haddasa barna.

Bugu da kari, mayakan sa-kai na Ansarullah suna ci gaba da kutsawa a cikin kasar Saudiyya a yankunan da su ke kan iyaka.

Fiye da shekara daya kenan dai Saudiyya ja shelanta yaki akan kasar Yamen, wanda zuwa yanzu ya ci rayukan dubban mutane da jikkata wasu dubban.