Kisan Kiyashin Saudiyya Da Safiyar Yau Juma'a A Kasar Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10468-kisan_kiyashin_saudiyya_da_safiyar_yau_juma'a_a_kasar_yamen
Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Mata Da Kananan Yara 9 A Yamen
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 02, 2016 01:58 UTC
  • Kisan Kiyashin Saudiyya Da Safiyar Yau Juma'a A Kasar Yamen

Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Mata Da Kananan Yara 9 A Yamen

A kalla mata da kananan yara 9 ne jiragen yakin Saudiyya su ka kashe da safiyar yau juma'a a kasar Yamen.

Tashar Telbijin din 'almasirah' ta kasar Yamen, ta ambaci cewa; da safiyar yau juma'a jiragen yakin Saudiyya sun kai hari a yankin "Baitu Maran" da garin "Arhab' da ke karkashin babban birnin kasar Sa'aa, wanda ya yi sanadin mutuwar mata hudu da kananan yara biyar.

Harin na yau, ya biyo bayan wani irinsa da jragen yakin Saudiyyar su ka kai a jiya alhamis a yankin Sa'aadh wanda ya yi sanadin mutuwar mutane16. Mafi yawancin wadanda su ka mutun dai kananan yara ne da mata.

Wasu jerin hare-haren na Saudiyya a jiya alhamis sun nufi cibiyar sadarwar ta waya a yankin Qahzah da ke karkashin Sa'adah. Sai kuma barikin soja na al-Saify, da kuma filin saukar jirgin sama da ke yammacin kasar ta Yamen.