Jamus : Kurdawa Sunyi Zanga-zanga Kyammar Erdogan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10546-jamus_kurdawa_sunyi_zanga_zanga_kyammar_erdogan
Rahotanni daga Jamus na cewa dubban kurdawa ne dake rayiwa a kasar suka gudanar wata zanga-zanga a yankin Cologne dake yammacin kasar domin nuna kyamma ga shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan bayan farmakin da sojojin Turkiyya suka kai kan Kurdawa a kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T11:28:52+00:00 )
Sep 03, 2016 17:31 UTC
  • Jamus : Kurdawa Sunyi Zanga-zanga Kyammar Erdogan

Rahotanni daga Jamus na cewa dubban kurdawa ne dake rayiwa a kasar suka gudanar wata zanga-zanga a yankin Cologne dake yammacin kasar domin nuna kyamma ga shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan bayan farmakin da sojojin Turkiyya suka kai kan Kurdawa a kasar Syria.

Ko baya ga hakan Kurdawan sun bukaci da a saki jagoran kungiyar PKK Abdullah Öcalan da hukumomin kasar Turkiyya ke tsare da tun cikin shekara 1999. 

Masu zanga-zangar na adawa da matakin mahukuntan Turkiyya a sahun gaba shugaba Erdogan musamen akan matakin da yake dauka tun dai bayan yunkurin juyin mulkin da baiyi nasara ba a kasar.

kanfanin dilancin labaren Jamus na DPA ya ce wannan zanga zanga ta hada mutane kimanin dubu talatin wanda ya yi daidai da adadin mutanen da kungiyoyin da suka shirya zanga zangar sukayi hasashe.

Bayanai daga yankin sun ce sun an gudanar da zanga zangar cikin lumana inda aka jibge dubban 'yan sanda don kaucewa duk wani abu da zai iya biyo baya.

Ko a ranar Juma'a data gabata wasu dalibai Kurdawa a lardin Grevenbroich dake arewacin kasar ta Jamus sunyi irin wannan zanga zanga wace ta rikide inda 'yan sanda uku da dalibai uku suka raunana.