Turkiyya Ta Bukaci Amurka Ta Cafke Fethullah Gülen
Mahukuntan Turkiyya sun bukaci Amurka data cafke malamin nan Fethullah Gülen dake gudun hijira a kasar bisa zarginsa da kisa juyin mulkin da baiyi nasara ba a kasar .
Ministan shari'a na kasar ta Turkiyya ne ya bukaci Amurka data cafke Gulen dake zaune a Amurka tun cikin shekara 1999, bisa zarginsa da shiryawa da kuma bada umurnin yin juyin mulkin da ya cutura a ranar 15 ga watan Yuli da ya gabata.
Wannan dai shi ne karon farko da mahukuntan Turkiyya suka nemi da a cafke shehu malamin dan shekaru 75.
Fethullah Gülen dai ya jima yana musunta duk wani hannu a yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Racep Tayib Erdogan.
Tun farko dai Turkiyya ta nemi Amurka data tuso mata keyar malamin, bayan da tura mata wasu takardu data ce Gulen nada hannu dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.