Harin Jiragen Yakin Saudiyya Akan Wata Makaranta A Yamen
Sep 14, 2016 02:49 UTC
Jiragen yakin Saudiyya sun kai hari a wata makaranta da ke yankin Sa'adah a kasar Yamen.
Jiragen yakin Saudiyya sun kai hari a wata makaranta da ke yankin Sa'adah a kasar Yamen.
Tashar telbijin din al-Masirah ta kasar Yamen, bada labarin cewa da safiyar yau laraba ne, jiragen yakin na Saudiyya su ka kai hari a yakin ali-Uqab da ke garin Sahhar a gundumar Sa'adah. Harin ya yi sanadiyyar rushewar makarantar baki dayanta.
Bugu da kari, jiragen yakin Saudiyyar sun ka wasu hare-haren a yankin Uddhal da ke birnin San'ah.
Fiye da shekara guda kenan da Saudiyyar ta shelanta yaki akan kasar Yamen, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma jikkata wasu da dama.
Tags