Saudiyya Tayi Maraba Da Yerjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11026-saudiyya_tayi_maraba_da_yerjejeniyar_tsagaita_wuta_a_siriya
Masarautar Saudiyya ta ce tayi maraba da yerjejeniyar tsagaita wuta a Siriya da kasashen Rasha da Amurka suka shata.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Sep 14, 2016 10:52 UTC
  • Saudiyya Tayi Maraba Da Yerjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya

Masarautar Saudiyya ta ce tayi maraba da yerjejeniyar tsagaita wuta a Siriya da kasashen Rasha da Amurka suka shata.

Saudiyya wace ke da dadaddiyar adawa da gwamnatin Bashar Al' Assad kana take goyan bayan 'yan tawayen Siriya ta ce tana maraba da yerjejeniyar wace ta tanadi rage wahalhalu ga al'ummar ta Siriya.

kakakin ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ya ce yana da muhimmanci gwamnatin Syria da 'yan tawayen kasar su mutunta yerjejeniyar.

A ranar Juma'a data gabata ce sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da Ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov suka cimma yarjejeniya tsagaita wuta a Geneva wace ta fara aiki a ranar Litinin data gabata.