Saudiyya Tayi Maraba Da Yerjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya
Sep 14, 2016 10:52 UTC
Masarautar Saudiyya ta ce tayi maraba da yerjejeniyar tsagaita wuta a Siriya da kasashen Rasha da Amurka suka shata.
Saudiyya wace ke da dadaddiyar adawa da gwamnatin Bashar Al' Assad kana take goyan bayan 'yan tawayen Siriya ta ce tana maraba da yerjejeniyar wace ta tanadi rage wahalhalu ga al'ummar ta Siriya.
kakakin ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ya ce yana da muhimmanci gwamnatin Syria da 'yan tawayen kasar su mutunta yerjejeniyar.
A ranar Juma'a data gabata ce sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da Ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov suka cimma yarjejeniya tsagaita wuta a Geneva wace ta fara aiki a ranar Litinin data gabata.
Tags