Babban Hafsan Sojin Rasha Zai Kai Ziyara Turkiyya
Sep 15, 2016 04:47 UTC
A wani likaci a yau din nan ne ake sa ran Babban hafsan sojin kasar Rasha Janar Valeri Guerassimov zai soma wata Ziyara a Turkiyya.
Wannan ziyara ta Janar Guerassimov nada nufin tattaunawa akan shawo rikicin kasar Siriya da kuma hadin gwiwa soji tsakanin kasashen biyu, a cewar wata sanarwa daga rundinar sojin kasar Rasha.
Haka zalika a wannan ziyara Janar Guerassimov zai gana da takwaransa na Turkiyya Hulusi Akar.
A kwanan bayan ne dai Kasashen Rasha da Turkiyya suka maido da hulda a tsakaninsu, bayan sabanin daya kunno kai lokacin da Turkiyya ta kakkabo wani jirgin sojin Rasha a iyaka da Siriya a cikin watan Nowamban bara.
Tags