Kashe 'Yan Koren Saudiyya Da Dama A Kudancin Kasar Yamen
Sojojin Kasar Yamen tare da dakarun Sa-kai, sun kashe 'yan koren Saudiyya masu yawa
Sojojin Kasar Yamen tare da dakarun Sa-kai, sun kashe 'yan koren Saudiyya masu yawa.
Tashar telbejin din al-masirah ta kasar Yeman ta bada labarin cewa; A jiya litinin sojojin kasar da dakarun Ansarullah sun kai hari akan 'yan koren Saudiyyar a yankin Kahbub da ke gundumar Lahaj a kudancin kasar, tare da kashe 14 daga cikinsu da kuma jikkata wasu 19.
Bugu da kari, sojojin na Yeman sun harba makami mai linzami akan sansanin soja na Sarki Khalid da ke yankin Khamis Mushaidh da gundumar Asir a cikin Saudiyyar.
Tun a cikin watan Maris na 2015 ne dai Saudiyyar ta shelanta yaki akan kasar Yeman, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka da dama.