Turkiyya : An Kori Jami'an leken Asiri 87
Gwamnatin Turkiyya ta kori wasu jami'an leken asiri kasar su guda 87 bisa tuhumarsu da alaka da shehun malamin nan Fethullah Gülen wanda ake zargi da kisa juyin mulkin da baiyi nasara ba a kasar.
Wannan dai shi ne karon farko da kasar ta kori jami'an leken asiri tun bayan yukurin juyin mulkin watan Yuli da bai yi nasara ba a kasar.
Gwamnatin Turkiyya dai na zargin Fethullah Gülen da shirya yuyin mulkin da ya cutura a ranar 15 ga watan Yuli wanda yayi sanadin mutuwar mutane 270 da kuma raunana dubbai.
Kuma tun lokacin gwamnatin Recep Tayib Erdogan ta dau matakin ba sani ba sabo kan duk wani da atek ganin yana da hannu a yunkurin juyin mulkin inda kawo yanzu ma'aikata kimanin 20,000 a fanni daban daban aka sallama daga bakin aikinsu.