Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Biya Turkiya Diyyar Dala Miliyan 20.
Sep 30, 2016 19:03 UTC
Jami'an gwamnatin Kasar Turkiya Sun Ce An biya Kasar Diyyar Jirgin Marmara
Tashar telbijin din cnn Turkey, ta bada labari a yau juma'a cewa; haramtacciyar kasar Isra'ila ta biya dala miliyan 20 a matsayin diyyar jirgin Marmara, da ta kaiwa hari a 2010.
Ministan makamashi da ma'adanai na kasar ta Turkiya Bar'at Biraq, ya ce; Tuni an zuba kudaden na diyya a cikin asusun ajiyar ma'aikatar shari'ar kasar.
A shekarar 2010 ne sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila su ka kai hari akan jirgin ruwan marmara na Turkiya wanda ya ke dauke da 'yan gwagwarmaya daga kasashe daban-daban da su ke kansu hanyu ta zuwa Gaza da aka killace.
'Yan kasar Turkiya 9 ne da ke cikin jirgin dai su ka yi shahada.
Tags