Turkiya: An Kashe Jami'an Tsaro 79 A cikin Watan Satumba
Kungiyar Kurdawa ta p.k.k ta kashe jami'an tsaron Turkiya 79 a cikin watan Satumba kadai.
Majiyar tsaron kasar Turkiya ta ce a cikin watan Satumba kadai, jami'an tsaron kasar 79 ne su ka mutu a hannun kungiyar Kurdawa ta p.k.k.
Kamfanin Dillancin Labarun Anatoly na Turkiya ya nakalto majiyar tsaron kasar na cewa; Hare-haren na kungiyar p.k.k ta dauki rayukan sojoji 49 da masu tsaron kauyuka, 28, sai 'yansanda 2, sannan kuma fararen hula 8. Bugu da kari majiyar ta ce wasu karin mutane 57 sun jikkata.
A gefe daya, majiyar ta ce; sojojin kasar sun kashe 'yan kungiyar p.k.k 1063 da kuma kame wasu 28. Sai kuma wasu 10 da su ka mika kansu da kansu ga mahukunta.
Sojojin na Turkiya dai suna fada da kungiyar ta P.K.K. a cikin gida da kuma kasashen makwabta, na Iraki da Syria.