Turkiyya : An Kama Dan Uwan Fethullah Gülen
'Yan sanda a Turkiyya sun kama wani dan uwa ga Shehun malamin nan Fethullah Gülen, wanda hukumomin kasar ke zargi da hannu a yunkurin yujin mulkin da baiyi nasara ba a kasar.
Kanfanin dilancin labaren Anatoli ya rawaito cewa an kame Kutbettin Gülen, a gidan wani makusancinsa dake yankin Izmir a yammacin kasar.
Ana dai zarginsa da kasancewa memba a kungiyar 'yan ta'adda mai dauke da makamai.
Rahotanni daga kasar sun nuna cewa an kwashi litafan Fethullah Gülen da dama a gidan mutiman.
Hukumonin Turkiyya dai na zargin shehun malamin Fethullah Gülen dake gudun hijira a Amurka da shirya juyin mulki wa gwamnatin Racep Tayib Erdogan a watan Yulin daya gabata wanda yayi sanadin mutuwar sama da mutane 270 da raunana wasu dubbai.
kuma tun lokacin ne gwamnatin Erdogan ta sanya kafar wando guda da duk wani da take ganin yana da hannu a yunkurin juyin mulkin inda kayo yanzu sama da ma'aikata 32,000 a fannonni daban daban aka kora daga bakin aikinsu.