MDD Ta Zargi Saudiyya Da Take Hakkokin Kananan Yara Da Mata
Kwamitin kare hakkokin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi kasar Saudiyya da take hakkokin kananan yara da mata budurwaye a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar Kwamitin kare hakkokin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniyan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ya fitar a yau din nan Juma'a inda ya bukaci gwamnatin Saudiyya da ta kawo karshen irin nuna bambanci da kuma take hakkokin mata budurwaye da take yi.
Sanarwar ta kara da cewa cikin mutane 47 da aka zartar musu da hukumcin kisa a watan Janairun wannan shekara ta 2016, hudu daga cikinsu ba su kai shekaru 18 ba a lokacin da aka zartar musu da hukumcin.
Har ila yau kuma kwamitin yayi Allah wadai da hare-haren da Saudiyyan take ci gaba da kai wa kasar Yemen lamarin da yake sanadiyyar mutuwar kananan yara da kuma mata masu yawan gaske a kasar.