Murabus na Gwamnatin Kuweit tare da rusa Majalisar Dokokin kasar
Bayan Murabus din Gwamnati da kuma rusa Majalisar Dokoki, Kuweit ta shiga yanayi na tsara zaben 'yan Majalisa.
A yayin da sabani ke kara karuwa tsakanin Gwamnati da Majalisar dokokin kasar Kuweit, A jiya Lahadi 16 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki, Gwamnatin Kuweit ta meka takardar yin murabus din ta ga Sarkin kasar, jim kadan bayan da ya karbi tare da amincewa na murabus din Gwamnatin, Sarkin kasar Kuweit Shekh Sabah Al-Ahmad ya sanar da rusa Majalisar dokokin kasar.
Rahotanni na cewa tushan musababin sabani tsakanin Gwamnati da Majalisar shi ne kara kudin Man fetun da Gwamnati ta yi, lamarin da ya sanya tada jijiyoyi na Al'ummar kasar da kuma wasu 'yan Majalisa , duk da cewa Gwamnati ta sha alwashin baiwa ko wani Dan kasar Lita 75 kauta, amma hakan bai kawo karshen sabanin ba.
Murabus din Gwamnati da kuma rusa Majalisar Dokoki a kasar Kuweit ba wani sabon abu ba ne, misali a yayin da Shekh Nasir Almuhamad ke rike a mikamin Piraministan kasar daga shekarar 2006 zuwa 2011, Gwamnatin ta kuweit ta yi murabus har so 7, a cikin wadannan shekaru biyar da Shekh Nasir Almuhamad ke rike da mikamin Piraminista, an rusa Majalisar Dokokin kasar har so uku. kuma an bayyana cewa dalilin da ya sanya hakan ta kasance yawan sabanin dake akwai tsakanin Majalisar Dokoki da Majalisar Zartarwa.
Daga watan Nuwambar 2011, Shekh Jabir Mubarak ya maye gurbin Shekh Nasir Almuhamad, sannan a watan Yunin 2013, Gwamnati ta shirya zaben 'yan Majalisa, bayan kafa Majalisar a karo na biyu Sarkin na Kuweit ya sake umartar Shekh Jabir Mubarak da kafa Gwamnati, inda Gwamnatinsa ta ci gaba da gudanar da milki a kasar har zuwa jiya Lahadi da ta yi murabus, A halin da ake ciki watanni 10 kacal ya rage da kawo karshen Majalisar Dokoki kamar yadda dokar kasar ta tanada, amma sai gashi a jiya Lahadi Gwamnati ta yi murabus sannan kuma sarkin kasar ya rusa Majalisar Dokokin.
Bisar dokar kasar ta Kuweit,wa'adin Majalisar Dokokin kasar shekaru hudu ne , ganin cewa an zabi Majalisar ne a watan yunin shekarar 2013, wa'adin Majalisar na karewa ne a watan yunin 2017.a zabe mai zuwa, tuni bangaren 'yan adawa suka bayyana shirin su na shiga a dama da su, babbar jami'iyar nan ta 'yan adawa da ake kira da Hadas ko kuma Jam'iyar 'yan uwa musulmi ta kasar Kuweit ta bayyana cewa bayan samun rinjaye a Majalisar dokokin a kasar tana sa ran za ta kafa Gwamnati.
Masu sharhin siyasar kasar na ganin cewa a kwai yiyuwar Sarki Shekh Sabah ya sake nada Shekh Jabir Mubarak a matsayin Piraministan rikon kwarya, to amma bayan gudanar da zaben 'yan Majalisa wajibi Gwamnatin dake miki ta yi murabus, amma Sarkin na Kuweit na da ikon sake nada Piraminstan da ya yi murabus ko kuma wani sabo na daban.