Saudiya ta saye Jirage marassa matuka daga Haramcecciyar kasar Isra'ila
Kafafen yada labarai sun watsa rahoton cewa magabatan saudiya na sayen makaman yaki daga Haramcecciyar kasar Isra'ila
A cikin rahoton da ya watsa ta hanyar shafinsa na Internet, Wani Dan Siyasar kasar Saudiya mai suna Mujtahid ya fayyace yarjejjeniyar da magabatan Saudiya suka kula na sayan makaman yaki tare da magabatan haramcecciyar kasar Isra'ila, daga ciki kuwa har da jiragen yaki marassa matuka, Mujtahid ya ce magabatan Saudiya sun watsa rahoton cewa za su gina kamfanin kera jiragen yaki marassa matuka a kasar Afirka ta kudu, wannan sanarwa yaudara ce daga magaban Saudiya domin a hakikanin gaskiya manufar watsa wannan sanarwa shine dauke hankulan Al'umma da kuma boye gaskiya a kan yarjejjeniyar da magabatan Saudiyan suka kula tare da HKI na sayar jiragen yaki marassa matuka ta hanyar kasar Afirka ta kudu na tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 400.
An kulla yarjejjeniyar ne a kan cewa Haramcecciyar kasar Isra'ilan za ta shigar da sasan jragen a kasar Afirka ta kudu a can kuma sai a hada su sannan kuma a shigar da su kasar ta Saudiya.Shakka babu a cikin watanin baya bayan nan masarautar Ali sa'oud tana mu'amala da KHI kai tsaye ko kuma ta bayan fage.misali a 'yan watanin da suka gabata tsohon shugaban Leken asirin Saudiya Turky Alfaisal ya gana da tsohon mai bayar da shawara a kan harakokin tsaron gida na HKI Ya'akub Amidur a birnin Watsinton na kasar Amurka inda suka tattauna kan alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma Siyasar gabas ta tsakiya.
Wannan sabon rahoto da aka watsa na alakar dake tsakanin magabatan Saudiya da HKI na zuwa ne a yayin da masarautar Ali-sa'oud ta umarci tsohon mai bayar da shawara a hukumar leken asirin kasar Anwar Ishki da ya bayyana irin kusanci da kuma alakar dake tsakanin masarautar Saudiya da Haramcecciyar kasar Isra'ila a siyasance ta yadda hakan ba zai kawo cece kuce a tsakanin kasashen musulimi da Larabawa ba, Tabbas wannan matsayi na magabatan saudiya na a matsayin cin amana ga kasashen musulmi da larabawa musaman Al'ummar yankin Palastinu wacce a ko wata rana take fuskantar zalinci da bakar siyasar HKI.a cikin 'yan watanin nan magabatan kasashen biyu sun gana a kasashe daban daban ciki kuwa har da HKI inda masarautar saudiyan ta jima tana bibiyar haramcecciyar kasar Isra'ila domin karfafa dangantar kut da kut dake tsakanin su musaman ma kan abinda ya shafi tsaro.
Masu sharhi kan harakokin Siyasa na ganin cewa wannan matsaya da magabatan saudiya suka dauka nada hadarin gaske ga kasashen musulimi musaman ma ganin cewa saudiyan na a matsayin babbar kasa kuma uwa ta kasashen musulmi da Larabawa,kuma Saudiyan za ta kasance tamkar mai zartar da bakar siyasar HKI ne a kasashen musulmi da Larabawa, wannan maudu'i ya janyo kakkausar suka daga Al'ummar musulmi na Duniya.
Sayan makaman da masautar Ali sa'oud ke yi daga HKI da kuma yadda magabatan HKI ke ci gaba da baiwa magabatan Saudiyan makamai na da mumunar manufa a kan kasashen yankin da kuma kasashen musulmi musaman ma idan aka la'akari da yadda wadannan kasashe ke ci gaba da taimakawa 'yan ta'adda a kasashen Siriya, iraki da kuma yadda kawancen saudiya ke ci gaba da ta'addanci a kasar Yemen.
A makunin da suka gabata, mahukuntan saudiyar sun bayar da umarnin sayan duban bindigogi da kuma milyoyin nau'i makamai ga 'yan ta'addar Siriya daga kasar Croatia, wannan labari ya fito ne daga bakin shugaban Hukumar Leken asirin Amurka wato SIA.
Shakka babu fadada alaka da Kasar Saudiya ke yi tare da HKI da kasashen Yamma gami da Amurka musaman ma ta bangaren tsaro na a matsayin rusa kasashen musulmi idan aka yi la'akari da yadda Hukumomin Leken asirin Amurka da na HKI tare da hadin kan magabatan Saudiya suka kirkiro kungiyoyin 'yan ta'adda tare basu mugayen makamai suka shigar da su kasashen musulmi kamar yadda ya wakana a kasashen Siriya, Iraki da kuma Libiya.